KIRKIRA
Mutane na korafi akan Facebook Messenger PIN
by admin on | 2022-12-16 06:34:26 Last Updated by admin on2026-02-22 10:30:21
Mutane dayawa suna ta magana akan wani (PIN) da ake turowa domin shigar da lambobin sirri akan shafin (Facebook Messenger PIN)
Wasu
suna zargin ta wannan hanya za a iya maka kutse wajen saka maka hotunan batsa ba tare da kasani ba.
Wani lokaci idan ka naimi bude sako kwatsam saikaga wannan alama ta neman lambar sirri, to sai dai gaskiyar magana wannan ba kutse bane.
Wannan alamar tana nuna cewa idan ka canja waya to tsoffin sakonnin ka zasu dawo akan sabuwar wayar daka canja ta hanyar shigar da wannan lambobi.
Tabbata ka shigar da (Password) mai karfi ta hanyar amfani da mabambantan harrufa da lambobi, sannan katayar da (two-factor-authenticator).
Idan kayi wadannan abubuwan dake sama to Insha Allah baka da matsalar kutse.